ABNA24 : A jiya Litinin ne dai hukumar nan ta General Services Administration da ke da alhakin amincewa da zababben shugaba ya fara gudanar da tsare-tsaren karbar mulkinsa a Amurkan ta sanar da Joe Biden din a hukumance cewa zai iya fara gudanar da ayyukansa na karbar mulki.
Shugabar hukumar Emily Murphy ce ta sanar da Mr. Biden din cewa a halin yanzu yana iya fara gudanar da ayyukansa na karbar mulki kuma hukumar a shirye take ta ba shi dukkanin abin da aka tanadar wajen gudanar da wannan aikin bayan a baya ta hana shi saboda shari’ar da ake yi kan sakamakon zaben a kotu in ji ta.
Hakan dai yana nufin kenan a halin yanzu Joe Biden zai sami kudaden da yake bukata wajen gudanar da wannan aiki daga gwamnatin tarayya kamar yadda kuma zai samu ofishin gudanar da wannan aiki bugu da kari kuma shi da mataimakiyarsa Kamala Harris za su dinga samun bayanan tsaro da na sirri daga wajen hukumomin tsaro na kasar a kai a kai.
Shugaba Trump din dai ya amince da wannan mataki da hukumar ta dauka duk kuwa da ya ce zai ci gaba da neman abin da ya kira hakkinsa da aka take masa yayin zaben a kotu.
342/